Journal statistics
How to use the archive
When the cursor changes from an arrow to a pointing finger, it indicates a link that you may click on to select that item.
The blue buttons at the top can be selected to return to the overview or to run a search for specific information.
Most volumes have been split into two parts, each with separate articles. When you select a specific number, all of the articles will be listed with details of the author, date of publication, language and the size of the file that will be downloaded if you choose that option. Just click on the yellow "Download" button to transfer a copy of the article to your own computer or device.
- Language Family: Chadic
- Topic #1: Historical Linguistics
- Topic #2: Phonology
Tsakure
Mujallar JWAL ta fara bayyana ne a shekar 1964. A wajen bukin cika shekaru 50 da fara wallafa wannan mujalla, wannan takarda da na gabatar ta hasko wani dogon tarihi na dangantaka tsakanin mujallar da harsuna ‘yan gidan Cadi. Takardar tana kira ga sake dawo da ɗabbaƙa nazarin kimiyyar harshe da ya shafi dangantaka ta tarihi tsakanin harsuna a Afirka, sannan kuma tana kira ga ɗalibai ‘yan Afirka da su mayar da ƙarfin bincike-bincikensu na ilmin kimiyyar harshe ya zama a kan kwatanta al’amura na tarihi tsakanin harsunan Afirka. Takardar tawa ta yi bayanai a taƙaice na kwatancin al’amuran tarihi tsakanin harsunan tsakiya na iyalan gidan Cadi kusan 80.Waɗannan harsuna su ne mafiya yawa daga cikin rukunai huɗu na harsuna ‘yan gidan Cadi a Afirka ta yamma. Haka kuma sun fi kowane rukuni yawan harsuna a cikin babban rukunin harsuna na Afroasiatic. Wasu muhimman bayanai da suka tuzgo, waɗanda kuma suka jiɓinci sake bibiyar tarihin ilmin tsarin sauti da fasalin ginin kalmomi a harsunan tsakiya na iyalan gidan Cadi, su ne fitattun alamomi na kashe-kashe kamar su fasalin ‘tushe-da-tsari’ da fasalin sassauƙan tsari na bai-ɗaya na tsarin wasula da rawar da ‘gishirin magana’ irin su ganɗantawa da wawuntawa da gunna da hamzantawa da bauɗewar tsarin tushe suka taka. Duka waɗannan sun ba da damar a fahimci yadda yawaitar tsaruka daban-daban na wasula ta samu a tsarin harunan na dauri da kuma yadda a yau aka sami shigowar sababbin baƙaƙe a harsunan, wanda kuma hakan shi ya sa harunan tsakiya na ‘yan gidan Cadi suka yi ƙaurin suna a samun bambance-bamabance a kamannin su.